Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna
ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV
cewa, Morgan Freeman yana hada wani shiri ne a tashar National Geographic a lokacin da yake amsa tambaya kan shirinsa
nasa wanda yake da alaka da Imani da ubangiji, sai ya bayyana cewa kiran salla
na daga cikin sautuka mafi kyau a duniya.
Ya ce ya yi bincike matuka dangane da lamrurran da suka shafi addinai, amma dangane da muslunci ya ga abubuwa na ban mamaki, daga ciki kuwa har da kiran sallah da musulmi suke yi a masallatai kafin fara salla, wanda acewarsa yana daga cikin sautuka mafi dadi da tasiri ga dan adama a duniya.
Ya ce yana son ya san yadda masu kiran sallah suke koyon yinsa kafin su fara shin suna halartar wani aji na musamman ne kan hakan?
A ranar 3 ga watan Afirilun 2016 ne aka watsa shirinsa a karin farko, ya zuwa yanzu an watsa bangare 6 daga cikinsa a talabijin.
A cikin muharram na wannan shekarar ne ya halarci taron Ashura a birnin London na kasar Birtaniya, inda yake ganewa idanunsa abin da ake gudanarwa, domin hakan ya taimaka masa a shirinsa.
Ya karbi kyautuka da daman a fina-finai, da hakan ya hada da kyautar oska a cikin shekara ta 2005, sai kuma a cikin shekara ta 2012 ya karbi kyautar wani fim na Golden Club wanda ya samu karbuwa a tsakanin Amurkawa.