IQNA

Hamas:
21:00 - November 25, 2016
Lambar Labari: 3480973
Bangaren kasa da kasa, Mahud Zihar daya daga cikin manyan jagororin kungiyar Hamas ya bayyana cewa, Isra’ila ba za ta iya hana kiran sallah a cikin yankunan Palastinawa ba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Mahmud Zihar a lokacin da yake gabbatar da jawabi a lokacin bude masallacin Aunbashi Hassan a ziriGaza, ya bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya hana musulmi gudanar da kiran sallah a yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma birnin Quds ba.

Ya ce kiran sallar da wani dan majalisa balarabe ya yia cikin majalisar dokokin Isra’ila babbar ushara ce kan hakan. Ya kara da cewa za a ci gaba da yin kiran sallaha dukkanin masallatai da ke cikin yankunan Palastinawa da Isra’ila ta mamayea cikin shekara ta 1948 ba tare da wani shayi ba.

Mahmud Zihar ya ce gina masallatai a cikin zirin gaza duk da irin barnar da yahudawa suka yi a yankin, wata manuniya ce ga Isra’ila, kan cewa ba isa ta iya hana muslmi gudanar da harkokinsu da suka shafi sallah da masallaci ba.

Sakamakon kafa dokar hana gudanar da kiran sallah da Isra’ila ta yi a wasu yankunan Palastinu da ke kusa da matsugunnan yahudawa da hakan ya hada har da birnin Quds, wasu daga cikin majami’oin kiristoci sun rika saka kiran sallah, domin nuna goyon bayansu ga musulmi.

3548690

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: