IQNA

23:46 - November 27, 2016
Lambar Labari: 3480977
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman ta’aziyyah na rasuwar marigayi Ayatollah Ozma Musawi Ardabili a birnin Istanbul na Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, cibiyar malaman mazhabar jaafariyya akasar Turkiya ta shirya gudanar da zaman ta’aziyyah dangane da rasuwar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Musawi Ardabili a birnin Istanbul na kasar.

An gudanar da zaman ne a yau bayan sallar magariba da Isha’i tare da halartar manyan malamai na mazhabar Ahlul bait a kasar.

An gabatar jawabai dangane da matsayin wannan bawan Allah da kuma irin hidimar da yay i addini ta fuskar ilmantarwa da tarbiyantar da malamai da dama.

Taron ta’aziyyar ya gudana a masallacin zainabiyyah da ke birnin Istanbul na kasar.

3549446


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: