IQNA

Gwamnatin Kenya Za Ta Shiga Kafar Wando Daya Da Makarantu Masu Yada Tsatsauran Ra’ayi

22:57 - December 03, 2016
Lambar Labari: 3480998
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Kenya ta sanar da shirinta na shiga kafar wando daya da makarantun da suke yada tsatsauran ra’ayin addini a gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya bayar da rahoto daga kasar Kenya cewa, gwamnatin kasar ta fara daukar matakai na bin kadun makarantun musulmi da ke yankunan arewa maso gabashin kasar, domin tantantace irin abubuwan da ake gudanarwa a cikinsu.

Muhammad Saleh wani jami’in gwamnatin kasar Kenya a bangaren kula da harkokin addinin muslunci a kasar ya bayyana cewa, makarantu da dama da suke yankunan arewa maso gabashin nkasar na musulmi ne, kuma an yi la’akari da cewa malaman da suke koyar da addini a makarantu mafi yawansu ‘yan kasar Kenya ba ne.

Ya ce baya ga hakan kuma, an la’akari da cewa da dama daga cikin masu shiga cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar ta Kenya suna fitowa ne daga irin wadannan makarantu, wadanda ake ganin cewa ana koyar da akidar tsatsauran ra’ayi da ke sa matasa shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda musamman kungiyar Alshaba, wanda hakan yasa dole ne a sanya ido a kana bin da ke faruwa awadannan makarantu.

Muhammad saleh daga karshe ya kirayi musulmin Kenya da su baiwa gwamnatin kasar hadin kai wajen zakulo da kuma tantance masu dauke da akidun ta’addanci da suke sake a cikin musulmi, suna aikata abubuwan da ke batawa musulmi da addinin muslunci suna.

3550456

captcha