Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran «Patriot News Agency» cewa, an gudanar da jin ra’ayin ne a cikin watan da ya gabata, kuma ya nuna cewa kashi 52 cikin dari na muuslmin kasar suna nuna cewa ba su san wanda ke da alhakin kai harin ba, amma kiman kashi 31 wato kusan kashi uku cikin dari, sun yi imanin cewa Amurka ce da kanta ta shirya lamarin, yayin da kashi 4 kuma suka dor alhakin kan alkaida.
To daya bangaren kimanin kashi 71 na mutanen kasr Birtaniya wadanda ba musulmi ba ne, suna ganin cewa alkaida c eke da alhakin kai harin, sai kuma kashi 10 cikin dari na ganin cewa George W. Bush ne ya shirya lamarin, amma kashi 1 kuma sun yi imanin cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta shirya harin na 11 ga satumba.
Musulmin kasar Birtaniya dai bisa kididdigar shekara ta 2011, sun kai kimanin miliyan 3 a Birtaniya, wato kimanin kashi 5 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar.