A cikin wasikar an bayyana cewa tun bayan zaben Trump, nuna kyama ga musulmi ya karu da kashi 115 a kasar Amurka, amma har yanzu Trump bai bayar da amsa kan wasikar ba.
A cikin makon da ya gabata ne aka kai farmaki kan wata 'yar sanda musulma mai suna Amal Sukari a yankin Bruklin na New York, inda ta fuskanci cin zarafi da kuma barazana kan rayuwarta.
Bill Dublasio gwamnan NewYork ya kira tare manema labarai, inda ya zauna wuri guda tare da Amal domin nuna takaicinsa kan abin da ya faru da ita, inda ya bayyana cewa babban abin bakin ciki ne yadda aka samu wasu Amurkawa suna nuna kyama ga ma'aikaciyar tsaro 'yar kasar Amurka saboda akidarta ta musulunci.
Ita ma anata bangaren Amal ta bayyana cewa, ita haifaffar kasar Amurka ce, amma addininta shi ne musulunci, kuma tana aiki ne kamar kowane dan kasa, kuma kowa yana bin addininsa da akidarsa kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasar, saboda haka suna bukatar Trump ya san matakin da zai dauka kan wannan lamari domin kare rayukan musulmi da dukiyoyinsu.