IQNA

Iran Na Gudanar da Baje Kolin Kayan Al’adun Muslunci A Afirka Ta Kudu

23:35 - December 26, 2016
Lambar Labari: 3481071
Bangaren kasa da kasa, ofishin jakadancin kasar Iran na gudanar da taron baje koli na kayyakin al’adun musulunci cibiyar Rasuli Center da ke birnin Pretoria akasar Afirka ta kudu.
Iran Na Gudanar da Baje Kolin Kayan Al’adun Muslunci A Afirka Ta Kudu

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na cibiyar yada al’adun muslnci cewa, ofishin jakadancin kasar Iran tare da babban ofishin kula da al’adun muslunci, sun bude wani babban baje koli kayyaykin al’adun muslunci, a cibiyar Rasuli da ke birnin Pretoria.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan baje koli ya samu karbuwa matuka daga mutane masu fahimta daban-daban daga cikin musulmi, kamar yadda kuma hatta ma wadanda ba msuulmi suna halartar wurin domin duba abubuwan da ake zuba.

Muhimman abubuwan da ake nunawa awurin dai sun hada da hotuna na wuraren tarihin muslunci, da kuma wasu abubuwa da suka hada al’adu daban-daban na al’ummar muslmi, gami da yadda musulmi suke cudanya da sauran al’ummomi na duniya.

Wannan baje koli ya zo ne daidai lokacin da mabiya addinin kirista suke gudanar da bukuwansu na kirsimati, inda ake nuna wasu abubuwa da suka hada bangarorin biyu.

Babbar manufar baje kolin dai ita ce kara kusanto da fahimta a tsakanin musulmi da kuma sauran al’ummomi da mabiya addinai daban-daban na duniya, ta yadda za a kara samun zaman lafiya da raywa tare da juna.

3556572


Iran Na Gudanar da Baje Kolin Kayan Al’adun Muslunci A Afirka Ta Kudu

Iran Na Gudanar da Baje Kolin Kayan Al’adun Muslunci A Afirka Ta Kudu
captcha