IQNA

Musulmin Manchester Sun Bayar Da Kyautukan Kirsimati Ga Marassa Lafiya

22:41 - December 29, 2016
Lambar Labari: 3481080
Bangaren kasa da kasa, musulmin birnin Manchester na kasar Birtaniya sun mika kyautuka na musamman ga yara marassa lafiyya domin murnan kirsimati.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Oldham Chronicle cewa, matasa musulmi mazauna wannan birni, sun bayar da kyautuka ga kananan yara da kwancea asibiti, da suka hada da kayan wasa, da kuma kayan zaki da littafai a bangaren kula da kananna yara marassa lafiya na asibitin birnin.

Laik Ahmad Khan ya bayyana cewa, babban burinsu shi ne suka sun faranta ma kananan yara kiristoci marassa lafiya rai, domin su yi murna kamar sauran yara kiristoci masu lafiya suke murna a wannan rana ta kirsimati.

Ya kara da cewa a kowane lokaci musulmi masu son zaman lafiya da sulhu da sauran al'ummomi da mabiya addinai daban-daban, musamman mabiya addinin kirista.

Inda yace anna Isa Almasih (AS) yana da matsayi na musamman mai girma a cikin addinin muslunci, saboda haka hatta musulmi suna murnar haihuwarsa.

3557640


captcha