IQNA

Dakin Karatu Na Charleston Zai Dauki Nayin Zaman Kan Musulunci

23:09 - January 01, 2017
Lambar Labari: 3481089
Bangaren kasa da kasa, babban dakin karay na garin Charleston a jahar Carolina ta kudu a kasar Amurka zai dauki nauyin wani zama domin tattauna lamurra da suka shafi muslunci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, shafin yada labaran na fitsnews ya bayar da rahoton cewa, wakilan babbar cibiyar msuulmi na kasar Amurka gami da wasu malamai da kuma masana msulmi za su halarci wannan zaman.

Babban abin da zai mayar da hankali a kansa shi ne sanin musulunci da koyarwa a kan batutuwa da suka shafi siyasa da zamantakewa, kamar yadda wasu daga cikin mahalar za su gabatar da tambayoyi domin wakilan msuulmi su amsa musu abubuwan da suka shige musu duhu dangane da addinin muslunci.

Wasu daga cikin Amurkawa masu tsananin adawa da addinin muslunci sun nuan rashin amincewarsu da hakan, inda suke ta yin rubuce-rubucen suka da batun a shafukan yanar gizo, amma masu kula da babban dakin karatun na Charleston sun yi watsi da hakan, inda suka bayyana mataki da cewa zai kara kusanto da fahimta tsakanin al’ummomin Amurka, musulmi da wadanda ba msuulmi ba.

Ita ma a nata bangaren bababr cibiyar musulmin Amurka ta yi lale marhabin da hakan, tare da yin fatar wannan ya zama wata hanaya da za ta kawo fahimta a tsakaninsu da masu mummunar fahimta a kan musluncia kasar ta Amurka.


captcha