IQNA

Bayanin ‘Yan Majalisa 191:

Kisan Ayatollah Nimr Ya Nuna Matukar Wawacin Mahukuntan Saudiyya

23:50 - January 03, 2017
Lambar Labari: 3481097
Bangaren kasa da kasa, majalisar Shawarar musulunci ta Iran ta fitar da bayani dangane da zagayowar cika shekara guda da shahadar sheik Nimr ali Nimr na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ‘yan majalisar dokokin kasar Iran 191 ne suka fitar da bayani wanda suka sanya hannu a kansa dangane da kisan gillar da mahukuntan masarautar ‘ya’yan gidan Saud suka yi babban malamin addini Ayatollah Baqir Nimr a shekarar da ta gabata.

Babban abin da bayanin majalisar ya kunsa

Ya yi tir da kisan da mahukuntan Saudiyyar su ka yi wa malamin na shi'a mai gwagwarmaya na kasar Saudiyya, sannan kuma ta zargi kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa da yin fuska biyu wajen mu'amala da zuriyar ali-Sa'ud.

Bugu da kari bayani wanda majalisar ta fitar a yau talata da ita ce ranar da malamin ya cika shekara guda da yin shahada, ya ci gaba da cewa; kashe Sheikh Nimr da ali-Sa'ud su ka yi a daidai lokacin da yankin gabas ta tsakiya ya ke fama da matsalar ta'addanci da rashin tsaro, yana nuni ne da rashin tsari da hangen nesa na ali-Sa'ud.

A ranar sha biyar ga watan oktoba na dubu biyu d sha biyar ne wata kotu a kasar Saudiyya ta yanke hukuncin kisa akan shehin malamin, ta hanyar fille kanshi da takobi sannan kuma a rataye gangar jikinsa a fili inda mutane za su gani."

An kuwa zarar da hukuncin kisar a kanshi ne a ranar biyu ga watan janairu na shekara ta dubu biyu da sha shida.

3559266


captcha