IQNA

Bahrain Ta Kashe Wasu Matasa Uku 'Yan Kasar Bisa Dalilai Na Siyasa

23:51 - January 15, 2017
Lambar Labari: 3481135
Bangaren kasa da kasa, Masarautar mulkin mulukiyya ta kasar Bahrain ta zartar da hukuncin kisa a yau a kan wasu matasa uku 'yan kasar, bisa zargin cewa sun tayar da bam da ya kashe wani dan sandan na kasar hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Jaridar Manama Post ta bayar da rahoton cewa, an kame wadannan matasa ne tun shekaru biyi da suka gabata, bisa tuhumar cewa suna da hannu a tayar da wani bam wanda ya kashe dan sandan hadaddiyar daular larabawa guda, daga cikin wadanda aka dauko haya domin murkushe zanga-zangar al'ummar kasar.

Kotun masarautar kasar ta yanke hukuncin kisa a kansu, bayan da aka azabtar da su tare da tilasta su amincewa da laifin da ake tuhumarsu, haka nan kuma masaratar Bahrain taki amincewa jami'an majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama su ji ta bakin matasan ba, lamarin da yasa shakku matuka a cikin zukatan masu bin diddigin lamarin.

Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, da suka hada da na Amurka da sauran kasashen turai, gami da Amnesty Int. da Human Rights Watch da sauran sun yi Allawadai da kakkausar murya kan wannan batu, tare da shan alwashin bin diddigin wannan lamari.

Fiye da kashi 80 cikin na al'ummar bahrain mabiya mazhabar shi'a ne, yayin da sauran da ba su kai kashi 20% ba, da suka hada da 'yan sunnah, da kuma kiristoci da 'yan abadiyyah, yayin da ita kuma masarautar kasar take bin tafarkin wakidar wahabiyanci.

Yanzu haka dai al'ummar kasar suna ci gaba da gudanar da gangami da jerin gwano a ko'ina cikin fadin kasar, domin nuna rashin amincewarsu da wannan mataki da suka kira na zalunci da kama karya.

3562953


captcha