Kamfanin
dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, A cikin wani bayani
da Nahad Awwad babban sakataren cibiyar musulmin Amurka ya karanta, ya bayyana
cewa suna kira ne da a dauki wannan mataki, domin tabbatar wa al'ummar Amurka
cewa Donald Trump bai amince da kyamar wani bangaren al'ummar Amurka saboda
addininsu, domin kuwa a cewar bayanin, idan wannan mutum ya halarci taron a
matsayin wanda aka gayyata, ya nuna cewa abin da yake daidai ne a hukumance.
Franklin Graham mutum ne da ke bayyana tsananin kiyayyarsa ga addinin muslunci da ma musulmi, inda a cikin shekara ta 2015 ya shelanta wani kamfe na kyamar msuulmi, tare da yin kira da a rufe dukkanin masallatai da cibiyoyi gami da makarantun msuulmia a kasar Amurka, saboda a cewarsa musulmi su ne 'yan ta'adda, kuma addininsu shi ne yake kira zuwa ga ta'addanci.
Haka nan kuma ya taka gagarumar rawa wajen yada kyamar musulmi a tsakanin al'ummar Amurka, musamman ma wadanda suke halartar majami'arsa ko kuma suke sauraren bayanansa.
A ranar 20 ga wannan wata ne na Janairu za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, yayin da wasu 'yan majalisa 10 na jam'iyyar Democrat suka haramta wa kansu halartar taron.