Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta CNN ta nakalto
daga jami'an 'yan sanda na birnin Washington cewa, ba su da shakku a kan cewa
abin da yafaru aiki ne na ganganci, amma ba su da wani dalili da za su iya
tabbatar da hakan.
Babban jami'in 'yan sanda na yankin Stew Melett ya bayyana cewa, hakai wutar ta yi barna matuka, domin kuwa ta nkone masallacin da kuma cibiyar musulmi da ke hade da masallacin, amma sun damke wani mutum mai suna Ishaq Wine William dan shekaru 37, wanda aka same shi a kusa da wurina lokacin da abin ya faru, kuma an sha samunsa da hannu wajen aikata laifuka na cutar da jama'a, a kan haka yana amsa tambayoyia hannun 'yan sanda.
A nata bangaren babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta bukaci jami'an tsaro da su gudanar da bincike na hakika a kan wannan batu, domin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin gurfanar da su.
Cibiyar ta kara da cewa, saboda yanayin da wurin yake ciki, an dakatar da dukkanin ayyuka a masallacin da kuma cibiyar da ke wurin har zuwa lokacin da za a kammala gyaransu.