IQNA

23:14 - January 18, 2017
Lambar Labari: 3481145
Bangaren kasa da kasa, Zuhair Magzawi wani dan majalisar dokokin kasar Tunisia ya bayyana kisan kan da masarautar Bahrain ta yi a kan mata 3 masu fafutuka da cewa sakamakon ne na yin shiru da duniya ta yi.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, jaridar Manama Post ta habarta cewa, Zuhair Magzawi shugaban jam’iyyar jama’ar Tunisia kuma dan majalisar dokokin kasar ya bayyana cewa, shirun da kasashen duniya suke yi kan kisan kiyashin da masarautar Bahrain take yi kan al’ummar kasar tun shekarun baya, shi ne kara mata karfin na yin kisan kai a kan matasa uku masu fafutuka a kasar.

A daya bangaren kuma kwamitin koli na kare hakkin bil-adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa kisan matasa ukku yan kasar Bahrain wanda gwamnatin Ali Khalifa suka yi baya bisa adalci.

kakakin hukumar ne ya bayyana haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, akwai wasu yerjeniyoyi wadanda kasashen duniya suka sanyawa hannu kan cewa sai an gabatar da wadanda ake tuhuma a gaban kotu sannan lauyoyinsa sun kare shi kafin a yanke masa hukunci ko wace iri ce.

Ya kara da cewa wadan nan matasa guda ukku wadanda gwamnatin kasar Bahrai ta bada sanarwan kashe su basu sami hukuncin adalcin da ya dace ba, kuma ba'a bawa lauyoyinsu damar kallon takardunsu ba. Bamda haka hatta iyayensu basu da labarin kan abinda ake tuhumarsu kafin su ji labarin an zartar da hukuncin kisa a kansu a ranar lahadin da ta gabata.

3563831


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: