IQNA

Aljeriya Ta Kafa Sbbin Dokoki Kan Shigo Da Kur’anai A kasar

23:37 - January 24, 2017
Lambar Labari: 3481165
Bangaren kasa da kasa, fira ministan kasar Aljeriya ya sanar da cewa sun kafa sabuwar doka dangane da shigo da littafai da kuma kur’anai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Alarabia cewa, Abdulmalik Salasil ya sanar da cewam daga yanzu babu wanda zai kara shigo da wasu littafai a kasar ko kuma wasu kwafin kur’anai, har sai ya samu izini daga hukma.

Ya ce bababr manufar kafa wannan sabuwar doka ita ce, tabbatar da cewa dukkanin littafan da ake shigo da su kasar ba su sabawa koyarwar abin da mutanen kasar suke a kansa ba, kuma ba za su kawo tashin hankali da tarwatsa hadin kan al’ummar kasar ba.

Tuni dai ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta kafa wani kwamiti wanda zai rika sanya ido ido kan harkokin da suka shafi tantace littafai da suke shigowa kasar, da farko za a duba littafin da kuma karanta shi domin ganin abin da ya kunsa.

Gwamnatin Algeria ta yi kashedin cewa, duk wanda ya sabawa wannan doka to zai fuskanci hukuncin da aka tana a kan haka.

3566138


captcha