IQNA

Sabon Salon Wani Mahaifi Na Koyar Da Diyarsa Kur'ani

22:24 - January 25, 2017
Lambar Labari: 3481170
Bangaren kasa da kasa, wani faifan bidiyo wanda ya zama daga cikin wadanda aka fi dubuwa a shafukan yanar gizo shi ne wani mahaifi da ke koyar da diyarsa kur'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa,a cikin faifan bidiyo an nuna wani amhaifi tare da diyarsa yana koya mata hanyar gane kure da kuma daidai a cikin karatun kur'ani, inda yake karanta ayoyi yadda suke daidai, daga bisani kuma sai ya karanta da kure, ita kuma tana gano kuransa.

Daga cikin abubuwan da da ya koyar da ita shi ne yin karatu da hukuncinsa na tajwidi, kuma takan gane idan an kure a wajen hada jumlolin kur'ani, ko kuma an tsallake aya, kamar yadda ta kan gane idan an kure a wajen hukunci na tajwidi.

Ko shakka babu wannan ya zama babban abin buga misali ga iyaye masu son su koyar da yayansua kan turba ta kur'ani mai tsarki, tare da koyar da su karatu da hukunsa.

3566613

captcha