Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga babban mai baiwa Donald Trump shawara kan harkokin tsaro Michael Thomas Flynn cewa, Trump yana da niyyar saka kungiyar ta 'yan uwa musulmi ta Masar a cikin kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya, wadanda kasar Amurka za ta shiga kafar wando daya da su.
Ya kara da cewa ko shakka babu wannan yana daga cikin abubuwan da gwamnatin Trump za ta aiwatar, amma bai san takamaimai lokacin da za t sanar da hakan a hukumance ba, wanda kuma hakan zai jawo takunkumin Amurka a kan kungiyar tare da rike kaddarorinta, da ma wasu matakan na daban.
Tun kafin wannan lokacin dai Donald Trump ya sanar da cewa zai aiwatar da dukkanin alkawullan da ya dauka na daukar kwararan matakai a kan abin da yake kira ta'addancin muslunci, tare da hana izinin shiga cikin Amurka ga wasu daga cikin kasashen musulmi.
Wasu daga cikin Amurkawa na ganain cewa saka kungiyar ta Muslim Brotherhood zai kara dagula alaka tsakanin Amurka da kasashen Turkiya da qatar, wadanda suke daukar nauyin kungiyar da kuma ayyukanta a ciki da wajen kasar Masar.