IQNA

Sabon Makirci Kan Ansarullah Na Yemen Da Sunan Rusa Masallatai

23:25 - January 28, 2017
Lambar Labari: 3481179
Bangaren kasa da kasa, gwamnati mai murabus da jami’anta ke gudun hijira sun bullo da sabon makirci na zargin mayakan kungiyar Ansarullah da rusa masallatai.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin labaran na Iram News cewa, Ahmad Attiyah ministan kula da harkokin addini na gwamnati mai mrabus a Yemen, a lokacin da yake ganawa da babban mai bayar da fatawa ga gidan sarautar yayan Saud kuma babban malamin wahabiyawa masu tsatsauran ra’ayi Abdulazizi Alusheikh, ya sheda masa cewa, mayakan kungiyar Ansarullah sun rusa masallatai da dama a kasar Yemen.

Inda ya sheda ma babban malamin wahabiyawan cewa Ansarullah sun rusa masallatai 299, yayin da suka lalata 24, kuma sun mayar da wasu masallatai 146 wurin ajiye makamai, inda suke amfani da su wajen kai hari a kan mayakan Hadi.

Kamar yadda ya saba Abdulazizi Alisheikh ya bayyana hakan a matsayin aikin wadanda yake kafirtawa da kisan su mushrikai, yana mai halasta abin da masarautar da yake baiwa fatawa take yin a kasha dubban musulmi a kasar Yemen mata da kanan yara, tare da bayyana haka a matsayin aikin wajibi.

Tun bayan da gwamnatin hadi ta yi murabus shi kuma ya tsere zuwa Riyadh, masarautar yayan Saud ta tilasta shi a kan ya janye murabus din da ya yi, duk kuwa da cewa wa’adin ulkinsa ya zo karshe domin ta fake da sunan mayar da shi kan mulki ta yaki al’ummar kasar Yemen kamar yadda take yi a halin yanzi a kan idanun al’ummomin duniya.

Ga dkkanin alamu ana son malamin wahabiyan ya bayar da fatawa ne da za ta tunzura musulmi kan sojojin Yemen da kuma mayakan ansarullah da aka fi sanu da Huthi, kamar yadda aka yi a kwanakin baya a lokacin da sojojin Yemen suka mayar da martani kan filin safka da tashin jiragen sama na birnin Jiddah babbar cibiyar kasuwancin masarautar yayan Saud, inda masarautar ta yi amfani da malamanta na wahabiyawan wa wajen bayyana cewa dakarun na Yemen sun harba makamin kan birnin makka ne, domin ta yi amfani da haka wajen tunzura musulmi da kuima halasta kisan mata da kananan yara da take yi a Yemen.

3567328


captcha