IQNA

16:54 - February 01, 2017
Lambar Labari: 3481191
Bangaren kasa kasa, an gudanar da wani zaman taro a kasar Tanzania wanda aka gudanar tare da hadin gwiwa da cibiyar Razawi kan zamantakewar al'umma.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan zama ne tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar ta Tanzania a birnin Darussalam fadar mulkin kasar.

Zaman taron wanda aka shirya shi bisa daukar nauyin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Darussalam ya samu karbuwa matuka daga mahalarta da kuam wadanda suka samu cikakken bayanin taron.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gabatar da jawabi kan muhimamncin da ke tattare da zamn lafiya a tsakanin al'ummomi da suke rayuwa atare ko da kowa suna da banbancin fahimta ta addini ko ta a'alad ko kuma akida.

Wanan taro ya gudana ne bisa koyarwa da kuma mahanga irin ta iyalan gidan manzo, wadda a kowane lokaci take girmama dan adam a matsayinsa na mutum wanda yake da kimar da Allah madaukakin sarki ya ba shi, wadda kuma wannan koyarwar limaman shiriya suka koyar da mabiyansu.

Daga cikin koyarwar iyalan gidan amnzon Allah a kan yadda suke kallon mutum shi ne, hadisin da aka karbo da sarkin muminai amincin Allah ya tabbata a gre shi, kuma limamai na farko daga limaman shiriya na iyalan gidan amnzo, wanda yake cewa, mutum dan uwanka ne ko dai a cikin addini ko kuma acikin hallita.

A bisa wannan akida da mahanga ta iyalan manzon Allah wadda ita ce hakikanin koyarwar addini da kuma gidan annabta, wadda take a matsayin babban ma'auni na zamantakewa da zaman lafiya a tsakanin bil adama.

3569329


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: