IQNA

16:50 - February 03, 2017
Lambar Labari: 3481197
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da janazar musulmin da suka yi shahada a lokacin da wani dan ta'adda ya bude wutar bindiga a kansu a lokacin da suke salla a cikin masallacin birnin Quebec na kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa dubban mutanen ne suka halarci janazar wadda a aka gudanara birnin Quebec, daga cikin wadanda suka harlarci janazar kuwa har da Firayi ministan kasar ta Canada Justin Trudeau.

Kafofin yada labaran kasar Canada da suka hada da gidajen talabijin na gwamnati da kuma masu zaman kansu sun watsa taron janazar kai tsaye, ta yadda miliyoyin mutanen kasar suka kalla, yayin da kuma fiye da mutane dubu 5 suka halarci.

Kimanin kwanaki biyar da suka gabata ne dai wasu 'yan ta'adda dauke da mayna bindigogi suka shiga cikin masalalcin Quebec a lokacin da ake sallar Isha'i, suka bude wuta akan masalla, a nan take mutane 6 suka rasa rayukansu, wasu kuma suka samu raunuka.

3569985


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: