IQNA

20:08 - February 07, 2017
Lambar Labari: 3481208
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taro da kuma bukin cika shekaru 38 da samun nasarar juyin jaya halin musulunci a kasar Iran a birnin Accra na kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya ce taron wanda sashen al'adu na ofishin jakdancin kasar Iran na birnin Acra ya shirya ya karfafa batun sulhuntawa da samun zamna lafiyaa duniya tare da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.

Jakadan Jamhuriyar Muslunci ta Iran a kasar Ghana Nasrullahi Maliki, a cikin jawabin da ya gabatar a taron ya bayyana cewa dole ne dukkan duniya ta taimaka don ganin an dawo da zaman lafiya da sulhin a duk fadin ta , ya kuma kara da cewa samun shuwagabanni Iran Imam Khomeni (RA) wanda ya assasa Jamhuriyar Muslunci ta Iran da kuma magajinsa Imam Aya. Sayyeed Ali Khamani'a ya taimaka korai wajen samar da zaman lafiya da kuma ci gaba a kasashen duniya.

Kasar Ghana na daga cikin kasashen da suke da kyakkayawar alaka da jamhuriyar muslunci ta Iran tun bayan samun nasasarar juyin juya halin islama.

Haka nan kuma wannan danganta ta ci gaba da habbaka inda kasar ta Iran take bayr da dukkanin taimako ga kasar a dkkanin bangarori na ci gaban ilimi da bunkasa ayyukan noma da masana'antun kasar.

Kasar Iran ta bude wasu makarantua kasar Ghana da suka hada da babbar jami'a ta muslunci, wadda take koyar da dukkanin bangarori na addini da kuma na kimiyya, wadda manyan malaman jami'oi a kasar ta Ghana suke koyarwa a cikinta.

Kamar yadda kuma Iran ta gina abubuwa da dama na ci gaban jama'a, da suka hada da taimaka wa wajen samar da wutar lantaki da kuma madatsun ruwa akasar, domin samun wadataccen ruwan sha da kuma noman rani.

Bayanin ya ce taron ya samu halartar malamai da masana da ma wasu daga cikin ‘yan siyasar kasar da kuma jami’an gwamnati, kamar yadda wakilan kungiyoyi masu kansu a kasar ta Ghana suka karba goron gayyatar da aka aike musu.

An girmama malamai da kuma wasu fitattun mutane na kasar ad suka halarci wannan taro na tunawa da zagayowar ranakun samun nasarar juyin juya halin muslunci.

3571102


Taron Samun Nasarar Juyin Juya Halin Muslunci A Iran A Kasar Ghana

Taron Samun Nasarar Juyin Juya Halin Muslunci A Iran A Kasar Ghana

Taron Samun Nasarar Juyin Juya Halin Muslunci A Iran A Kasar Ghana

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: