IQNA

20:14 - February 07, 2017
Lambar Labari: 3481210
Bangaren kasa da kasa, wani mutum dan Saudiyya da aka bayyana cewa yana fama da tabin hankali ya so cinnawa zanen dake lulube da masallacin Ka'aba mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, rahotanni daga Saudiyya sun ce tun da farko mutumin ya banka ma kansa man fetur ya kuma cinnawa kansa wuta kafin daga bisani ya nemi ya rabaga zanendake lullube da masallacin Ka'aba.

Bayanai daga kasar sun ce jami'an tsaro masallacin sunyi nasara kauda barazana mutumin dan kimanin shekaru arba’in kafin ya kai ga cimma manufarsa kamar yadda kakakin 'yan sanda masallacin ya samnar ga manema labarai.

'Yan sanda dai sun bayyana mutimin a matsayin mai tabin hankali, aman wasu rahotanni na daban sun ce mutimin ya yi ta kabbara irin ta 'yan ta'adda.

3571707Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Saudiyya ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: