IQNA

Jagoran Juyin Islama:
22:55 - February 08, 2017
Lambar Labari: 3481211
Bangaren kasa da kasa, A ganawar da yayi da kwamandoji da manyan jami'an rundunar sojin sama ta Iran da na sansanin kare sararin samaniyyar kasar Iran a jiya Talata, Jagoran juyin juha halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya mayar da martani ga kalaman baya-bayan nan da sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi kan Iran yana mai bayyanar da hakikanin siyasar yaudara ta Amurkan.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA ya habarta cewa, A yayin wannan ganawar wacce aka yi ta don tunawa da ranar da jami'an sojin sama na Iran suka yi wa marigayi Imam Khumaini (r.a) mubaya'a a ranar 8 ga watan Fabrairun 1979 ('yan kawanaki kafin samun nasarar juyin juya halin Musulunci) Ayatullah Khamenei yayi ishara da kalaman shugaban Amurkan Donald Trump da ke cewa wajibi ne Iran ta gode wa tsohon shugaban Amurka Barack Obama saboda abin da ya kira daga kafar da yayi wa Iran ta inda ya ce sabon shugaban Amurkan ya tabbatar wa duniya da hakikanin Amurka wanda tsawon shekaru talatin da wani abu Iran take fadi. Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa hakan wani lamari ne da ke nuni da cewa babban kuskure ne a dogara da shaidanu da kuma mutanen da suke adawa da asalin tsarin Musulunci da kuma iko na Musulunci a kan al'umma.

A halin yanzu dai shekaru 38 kenan da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, tsawon wannan lokaci dai babu wani lokaci da al'ummar Iran suka taba yarda da kuma amincewa da dabi'u da kuma siyasar Amurka. A saboda haka ne ma tunanin cewa akwai wani bambanci tsakanin halaye da dabi'un Barack Obama ko wani shugaban Amurka na daban a kan Iran, tunani ne da ke cike da kuskure da kuma rashin fahimtar hakikanin siyasar Amurkan. Wadannan maganganu da halaye na sabon shugaban Amurkan wani lamari ne da ke nuni da siyasar Amurka a baya da kuma a halin yanzu, wata siyasa ce guda daya. A saboda haka ne ko a lokacin mulkin Obaman, wanda kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fadi ya mika hannun abokantaka wa Iran alhali a boye kuma yana ci gaba da gudanar da siyasar cutar da Iran din, al'ummar Iran ba su rudu da irin wannan sakin fuska ta zahiri ta Obaman ba, ballantana a halin yanzu Trump din yayi tunanin cewa suna cikin damuwa ko kuma kamar yadda ya ce wajibi ne su gode wa gwamnatin Obaman.

Idan da Trump zai dan yi dubi a baya kadan da kuwa zai ga cewa gwamnatin Obaman ba wai ta raga wa Iran ba ne face dai ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen kiyaye matsayin Amurkan sannan kuma har gwamnatin ta tafi tana ci gaba da maganar yiyuwar amfani da karfin soji a kan Iran. Hatta a ranakun karshe-karshen na mulkinsa, Obaman ya sanya hannu kan sake sabunta takunkumin shekaru goma da aka sanya wa Iran wanda da dama suke ganin hakan a matsayin wani share fage ne ga Trump din na ya ci gaba siyasar adawa da Iran da siyasar Amurkan ta ginu a kai.

Duk da cewa gwamnatin Obaman ta dare karagar mulki ne da taken kawo sauyi, sannan kuma duk da ikirarin da yayi na cewa gwamnatocin Amurkan da suka gabata sun yi kuskure a kan Iran musamman rawar da Amurkan ta taka wajen kifar da halaltacciyar gwamnatin Iran ta Dakta Mosaddiq a shekarar 1953 da kuma goyon bayan Saddam da tayi a yayin kallafaffen yaki, to amma a zahiri babu wani abin a zo a gani da yayi wajen gyara wadannan kura-kurai hatta yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da Iran wacce a saboda ita din ce Trump din yake cewa wajibi ne Iran ta gode masa, amma yayi hakan ne don kiyaye mutumcin Amurkan kawai ba wai saboda Iran ba.

A saboda haka abin da yake a fili shi ne cewa idan ma har sabon shugaban Amurkan yana son sake bayyanar da siyasar adawa da Iran a fili ne, to tamkar wadanda suka gabace shi ba zai yi nasara ba, don kuwa a wajen al'ummar Iran babu wani bambanci tsakanin Amurkan Trump da Amurkan sauran shugabannin Amurkan da suka shude tsawon shekaru 38 din da suka gabata. Don kuwa tsawon wadannan shekaru 38 babu wani abin da al'ummar Iran suka gani daga wajen wadannan shugabanni na Amurka in ban da gaba da kiyayya, amma hakan bai hana su ci gaba da riko da tafarkin da suka rika ba. Don haka a wannan karon ba sabuwar gwamnatin ba za ta sanya su juyawa da baya daga wannan tafarki na su ba.

3571779


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: