IQNA

23:42 - February 08, 2017
Lambar Labari: 3481212
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin jahar Lagos da ke tarayyar Najeriya ta sake dawo da batun hana dalibai mata a makarantun firamare da sakandare saka hijabi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Nigerian Bulletin ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin jahar Lagos ta sake dawo batun hana dalibai saka hijabi a makarantu, inda ta mika batun ga kotun koli, bayan da wata kotun daukaka kara ta yi watsi da dokar, tare da bayyana hakan a matsayin tauye hakkokin dalibai mata musulmi.

Gwamnatin jahar Lagos dai ta fake ne batun matsalar tsaro a arewa maso gabashin Najeriya, inda take bayyana cewa saka hijabi a makarantu zai iya zama barazana ta fuskar tsaro.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a Lagos da kuma kungiyoyin mata musulmi sun kakkausar suka dangane da wannan mataki na gwamnatin jahar, tare da shan alawashin bin dukkanin hanyoyi na shari'a domin kalubalantar wannan doka.

3572370


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: