IQNA

23:15 - February 09, 2017
Lambar Labari: 3481214
Bangaren kasa da kasa, sarkin Kano ya sanar da shirin da ya kamata a mayar da hankalina kanta ta fuskar koyarwa a masallatai.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, shafin jaridar punchng ya habarta cewa, Sanusi Lamido sanusi sarki Kani ya bayyana cewa, ya zama a fara aiwatar da sabbin shirye-shirye na ilmantarwa a cikin masallatai.

Sarki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar wani taron yaye wasu malamai su kimanin dubu biyu, inda ya bayyana hakika babban aikin da ke a gaban malamai shi ne su mike tsaye su amfani da dkkanin damar da suke da ita wajen ilmantar da jama’a a dukkanin bangarori na rayuwa.

Ya yi ishara da cewa, a wasu kasashe kamar kasar Moroco ana yin amfani da masallatai ba kawai domin salla ba, akan gudanar da shirye-shirye na ilmantar da jama’a dangane da lamarin addininsu da kuma yadda ya kamata su fskanci rayuwarsu ta zamantakewa da sauransu.

A kan sarki ya ce irin haka ne ya kamata a mayar da hankali a kansa domin al’ummar arewa ta zamaa cikin fadaka da sani lamrarin addininta da kuma duniyarta, domin kuwa a cewarsa ta fuskar book kud sun wuce arewa, amma hakan bay a nfin cewa arewa ba za ta iya yunkurawa ba ne, kowa yana da gudunmawar da zai bayar domin ganin al’ummarsa ta arewa ta samu ci gaba.

3572246


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: