IQNA

23:20 - February 09, 2017
Lambar Labari: 3481216
Bangaren kasa da kasa, Jami'an gwamnatin kasar Jamus na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da irin salon siyasar shgaban kasar Amurka Donald Trump.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, wasu daga cikin kafofin yada labaran kasar Jamus sun bayyana cewa tun abyan da Donald Trump ya sanya hannu a kan dokar hana musulmi daga kasashe bakawai da kuma 'yan gudun hijira shiga kasar Amurka, mafi yawan jami'ai da kuma 'yan siyasa na kasar ta Jamus suka sanar da raba gari tsakaninsu da irin wannan salon siyasa.

Wani abu na biyu kuma wanda ya kara bakanta ran mahukunta a kasar ta Jamus shi ne cin zarafin da jami'an tsaron Amurka suka yi wa wani dan majalisar dokokin kasar ta Jamus wanda asalinsa dan kasar Iran, tare da hana shi shiga cikin kasar ta Amurka, lamarin da ya sanya shugabar gwamnatin kasar ta Jamus ta fito ta yi kakakusar suka a kan salon siyasar Trump.

Tun bayan faruwar wannan lamari yanzu haka dai 'yan majalisa a kasar ta Jamus baya ga yin kalamai na suka a kan gwamnatin Trum, suna shirin daukar wasu matakai na mayar da martani kan cin zarafin da Amurka ta yi wa wannan dan majalisa.

3572489


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Jamus ، majalisa ، Amurka ، Donald Trump
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: