IQNA

22:25 - February 12, 2017
Lambar Labari: 3481223
Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen makaranta da kuma mahardata da za su halarci gasar kur'ani ta duniya da az a gudanar a kasar Iran daga Tanzania.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, ofishin jakadancin kasar Iran daga Tanzania ya sanar da cewa, yanzu haka an kammala dukkanin aikin tantance makaranta da kuma mahardata daga kasar at Tanzania da za su halrci gasar karatu da hardar kur'ani ta duniya da za a gudanar a kasar Iran.

An gudanar da tantancewar ne a wata gasa ta cikin gida da aka shirya, inda daruruwan makaranta suka taru suka gudanar da karatu a dukkanin bangarorin da za a gudanar da gasar, an kuma tantance wadanda za su halarci gasar a kowane bangare.

Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin wadanda suka halarci gasar sun hada da mayna jami'an gwamnati musamman a bangaren kula da harkokin addini a kasar, sai kuma jami'an huldar diplomasiyyar kasar Iran da suke a kasar.

Daga cikin irin abubuwan da aka gudanar kuwa har da sauraron karatu da kuma yadda mai karatun yake kiyaye kaidoji da kuma yanayin sautinsa da lahanin sauti, kamar yadda kuma a bangaren harda ana la'akari da saurin fahimtar aya da aka karanta da kuma yadda mai karatu zai ci gab aba tare da wata matsala ba, kamar yadda kuma aka yi la'akari da yawan kura kurai ko karancinsua cikin karatu da kuma harda.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron, jakadan kasar Iran ya bayyana cewa, manufar karatu ko hard aba ita sanin kaidojin karatu ko hardace ayoyin kur'ani ba, babbar manufa it ace sanin abin da ake karatawa da kuma aiki da shi.

Kamar yadda kuma ya yi ishara da shirin da aka kaddamar a karkashin jagorancin Imam Khamenei na samar da mahardata kur'ani mai tsarki miliyan 10 a cikin jamhuriyar muslunci da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi, wanda kuma da yardar Allah kasar ta Tanzania za ta kasancea sahun gaba wajen shiga cikin wannan shiri.

Daga cikin makaranta da kuma mahardata kur'ani na kasar da suka samu dama da kuma cancantar halartar gasar kur'ani ta duniya ajamhuriyar muslucni ta Iran akwai, Abdulhamid masu'ud a bangaren harda, Adam Juma'a a bangaren karatu, Arifah bin Hussain, a bangaren karatu, Suriya Ali a bangaren harda.

Kasar Tanzania dai ta kasance daya daga cikin kasashen Afirka da Iraniyawa suke zaune a cikinta, domin kuwa akwai mutanen Shiraz da suka kwashe daruruwan shekaru suna rayuwa a kasar Tanzania kuma sun zama 'yan kasa.

3573496


An Sanar Da Sunayen Wadanda Za Su Halarci Gasar Kur'ani Ta Daga Tanzania

An Sanar Da Sunayen Wadanda Za Su Halarci Gasar Kur'ani Ta Daga Tanzania

An Sanar Da Sunayen Wadanda Za Su Halarci Gasar Kur'ani Ta Daga Tanzania

An Sanar Da Sunayen Wadanda Za Su Halarci Gasar Kur'ani Ta Daga Tanzania


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: