IQNA

22:28 - February 12, 2017
Lambar Labari: 3481224
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a birnin Tennessee da ke kasar Amurka sun gudanar da wani shiri domin kara wayar da kan mutane dangane da koyarwar kur'ani.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin Times Free Press ya habarta cewa, an gudanar da wannan shiri ne a jiya a babbar cibiyar muslunci da ke birnin, inda aka baje kwafi-kwafi na kur'ani da suka hada da wadanda aka tarjama a cikin harshen turanci.

Babbar manufar hakan dai ita ce wayar da kan mutanen birnin dangane da koyarwar kur'ani, da kuma amsa tambayoyinsu kan matsalolin da suke da su da suka shafi muslunci da kuma kur'ani mai tsarki.

Mutane da dama sun halarci da suka hada mabiya addinai daban-daban musamman dai mabiya addinin kirista, inda aka nuna musu kur'ani da kuma wanda ak atarjama a cikin harshen turanci, tare da yi musu bayani kan hakikanin abin da wannan littafi mai tsarki yake koyarwa.

Mahalarta wurin sun rika gabatar da tambayoyi kan abubuwa da suka shige musu duhu dangane da addinin muslunci, inda aka rika amsa musu tambayoyin da kuma basu misalai daga kur'ani mai tsarki.

Duk da cewa wannan shi ne karon farko da cibyar take gudanar da irin wannan shiri, amma ya kayatar matuka, inda mutanen ad suka halarci wurin suka nuna gamsuwa matuka da irin karamcin da musulmi suka nuna musu, tare da yin kira da a ci gaba da gudanar da irin wannan taro na wayar da kan mutane dangane da addinin muslunci.

3573639


Samun Masaniya Kan Kur'ani A Cibiyar Musulmi Da Ke Tennessee Amurka

Samun Masaniya Kan Kur'ani A Cibiyar Musulmi Da Ke Tennessee Amurka

Samun Masaniya Kan Kur'ani A Cibiyar Musulmi Da Ke Tennessee Amurka

Samun Masaniya Kan Kur'ani A Cibiyar Musulmi Da Ke Tennessee Amurka

Samun Masaniya Kan Kur'ani A Cibiyar Musulmi Da Ke Tennessee Amurka


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Tennessee ، Amurka ، addinai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: