IQNA

Hukuncin Tara A Kan Wani Mai Cin Zarafin Musulmi A Birtaniya

21:41 - February 14, 2017
Lambar Labari: 3481229
Bangaren kasa da kasa, An ci wani mutum tarar kudi har fan 335 da ke cin zarafin musulmi a kasar Birtaniya ta hanyar yin zane-zanen batunci a bangaye da nufin muzguna wa musulmi.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Shafin asianimage ya habarta cewa, Stefan Gray dan shekaru 54 da haihuwa wanda ke aikin zane-zane yana yin amfani da damarsa ta aiki wajen yin zane a kan bangaye inda yake yin zanen batunci a kan musulmida addinin muslunci.

Wajid Hussain wani musulmi ne mazaunin birnin Blackburn na kasar Birtaniya, wanda kuma shi ne ya kai karar Stefan Gray, bayan da ya yi zanen batunci ga musulmi a kan bangon gidansa.

Alkalin koton birnin ya gamsu da dukkanin hujjojin da Wajin Hussain ya gabatar dangane da abin da mutumin ya aikata, baya ga haka kuma wasu daga cikin mazauna birnin sun bayar da sheda makamncinyar hakan a kansa.

Adadin musulmi a kasar Birtaniya bisa kididdigar shekara ta 2011 ya kai miliyan 2.7, akasarinsu kuma sun fito ne daga kasashen India, Bangaladash da kuma Pakistan.

3574562


captcha