IQNA

23:17 - February 15, 2017
Lambar Labari: 3481234
Bangaren kasa da kasa, babban kwamitin kula da harkokin musulmin kasar Amurka ya yi lalae marhabin da murabus din da General Michael Flynn babban mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro ya yi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, kwamitin kula da harkokin musulmin kasar Amurka ya bayyana murabus din da Michael Flynn babban mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro ya yi da cewa babban ci gaba ne, tare da fatan wasu masu irin ra’ayinsa da suka kewaye shugaban su za su yi hakan.

Fadar shugaban kasa ta white house ta tabbatar da wannan labarin ta kuma kara da cewa tuni an maye gurbinsa da Keith Kellog wani janaral na sojojin Amurka mai ritaya.

Labarin ya kara da cewa Flynn ya ajiye aikin nasa ne a jiya litinin ya kuma gabatar da uzurinsa ga shugaban kasa da kuma mataimakinsa kan kuskuren da yayi na shaida masu ba dai dai ba kan dangnatarsa da jakadan kasar Rasha a Amurka tun kafin zuwa gwamnati mai ci.

Flynn ya ajiye aikinsa ne jim kadan bayan da aka fara watsa labari kan cewa ma'aikatar shari'ar kasar ta yi gargadi wa shugaba Trump da yayi hankali da Flynn din don yana da dangantaka ta kud da kud da jakadan kasar Rasha A Amurka. Kuma rahoton da ya bayar na musanta hakan ba gaskiya bane.

3574964


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ، litinin ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: