IQNA

21:49 - February 17, 2017
Lambar Labari: 3481239
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta mayar da martani dangane da gargadin da Sayyid Hassan Nasrullah ya yi mata kan tashoshinta na nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, a jawabin da Sayyid Nasrullah ya gabatar a yammacin Alhamis da ta gabata, ya gargadi Isra’ila da cewa, bayan kwashe makama da kuma sanadarai na nukiliya daga Amuniyak da ke Haifa, to su hada da makaman nukiliyarsu da ke cibiyar Dimona.

A cikin jawabin nasa Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana kasantuwar makaman nukiliya na Isra’ila a wadannan wurare a matsayin wata babbar dama ga mayakan Hizbullah a duk lokacin da Isra’ila ta yi gigin shiga wani sabon yaki da su.

Wannan furuci ya bakantawa jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila matuka, inda ministan liken asirin Isra’ila Yisrael Katz ya fito ya bayyana cewa, idan nasrullah yana da karfin da zai kai hari a kan cibiyoyi da muhimman wurare a cikin Isra’ila da makamai masu linzami, ita kuma Isra’ila tana da karfin da za ta kai hari a ko’ina a cikin kasar Lebanon.

3575283


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: