IQNA

23:32 - February 19, 2017
Lambar Labari: 3481246
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar da ke kula da harkokin msuulmi a kasar Amurkka ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da barazanar kisan musulmi da wasu suka yi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, shafin wral ya bayar da rahoton cewa, wasu masu tsananin kiyayya da addinin musulunci a kasar Amurka sun gudanar da wani zaman taro a jahar Carolina ta arewa da suka hada har kungiyar nan ta TParty mai tsananin kyamar musulmi, inda wasu daga cikinsu suka bayar da shawar kan kasha musulmi.

Wannan babbar cibiyar musulmi ta bayyana wannan barazana da cewa tana da matukar hadari, kuma hakan yana a matsayin wani babban laifi bisa dokokin kasar Amurka, a kan hakan cibiyar ta bukaci hukumar ‘yan sanda ta FBI da ta gudanar da bincike kan wannan lamari.

Zaman da kungiyoyin suka gudanar, an yi shi ne bisa take yiwuwar musulmi suka wo ma Amrka hari, inda wasu suka ce ya kamata a dauki mataki tun kafin haka ta faru a kasha dukkanin musulmin da suke cikin Amurka.

Tun bayan da kungiyoyi masu kyamar musulmi suka fara bulla a cikin kasar Amurka a yan shekarun baya-bayan nan, ake ci gaba da samun karuwar barazana a kan musulmi, yayin da a wasu wuraren ma har ana kai musu ana kone musu masallatai.

Ga dukkanin alamau lamarin zai ci gaba da kara bazuwa, ganin cewa sabuwar gwamnatin Amurka ta zo a kan ulki ne bisa ra’ayi mai kama da haka na kyamar msuulmi.

3575873


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: