IQNA

23:03 - February 28, 2017
Lambar Labari: 3481269
Bangaren kasa da kasa, wata bafalstiniya mai suna Sa’adiyyah Aqqad ta rubuta cikakken kur’ani mai tsarki wanda ya dauke ta tsawon shekaru uku.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga jaridar Almisriyun cewa, Sa’adiyyah Alaqqad ta rubuta kur’anin ne tana da shekaru 24 da haihuwa aduniya, bayan kammala karatu a jami’ar Khan Yunus da ke yankin zirin Gaza.

Bayanin ya ci gaba da cewa ta fara wanna aikin ne tun a cikin shekara ta 2014, kuam ta ci gaba da bayar da himma a kan aikin da dukkanin lokacinta, inda daga karshe ta samu nasarar kammala wannan aiki mai matukar kima da matsayi.

Haka nan kuma ta bayyana cewa ta gudanar da wannan aikin ne ba domin wani abu ba, sai domin neman yardar Allah, kuma ta yi hakan ne ta mai fatan Allah ya kai ladar ga dukkanin wadanda suka shahada a zirin Gaza sakamakon hare-haren yahudawan sahyuniya.

Dangane da yadda ta gudanar da aikin kuwa ta bayyana cewa, ita kadai ce ta yi wannan aiki ba tare da neman taimakon kowa ba, hatta tsarin talardun da kuma yadda ta yi zane a kan takardun da take rubta ayoyin kur’ani mai tsarki a cikinsu it ace ta nemi kalolin da suka dace kuma ta yi zanen da kanta.

Ta bayyana cewa ba ta taba halartar wani aji domin koyon rubutun kur’ani ba, ta koya ne don kashin kanta tare da taimakon Allah madaukakin sarki, kamar yadda kuma babu wta ma’aikata ko wata cibiya da ta taimaka mata da kudi domin wannan aiki.

Ta kamala rubutun kur’anin mai shafuka 522m wanda kuma yanzu haka tana tattaunawa tare da ma’aikatar kula da harkokin addini a Gaza domin yin nazari kan kur’anin da kuma tabbatar da cewa an gyara kura-kurai idan har an same su kafin amincewa a yi amfani da shi.

3579123


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: