IQNA

An Fara Babban Taron Kur'ani Mai Taken Said Bin Jubair A Iraki

23:33 - March 08, 2017
Lambar Labari: 3481294
Bangaren kasa da kasa, a yau laraba an fara gudanar da taro kan kur'ani mai tsarki a lardin Wasit na kasar Iraki mai take Said bin Jubair.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, shi dai wannan taro an fara gudanar da shi ne a ne a yau a garin Kut baban birnin lardin Wasit na kkasar Iraki.

Wannan taron yana samun halartar makaranta kur'ani mai tsarki da kuma masana kan ilmomin kur'ani daga kasashe 20, inda ake gabatar da jawabai da kuma karatu a dukkanin bangarori na harda da kuma kira'a gami da tafsirin kur'ani mai tsarki da dai sauransu.

Manufar gudanar da wannan taro dai ita ce tunawa da wannan bawan Allah wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimin addinin muslunci musamman tafsirin kur'ani mai tsarki daidai da mahangar manzon Allah da iyalan gidansa masu tsarki.

Shi dai wannan bawan Allah Said Bin Jubair bin Hashim Alasadi, ya kasance daya daga cikin sahabban Imam Sajjad (AS) wanda ya samu ilimi sahihi daga wannan gida mai tsarki, ya kasance mahardacin kur'ani kuma babban mai tafsirin kur'ani mai tsarki bisa ruwayoyin ahlul bait amincin Allah ya tabbata a gare su.

A cikin shekara ta 95 bayan hijirar manzon Allah (SAWW) ya yi shahada a hannun Hajjaju bin Yusuf Al-thaqafi, daya daga cikin azzaluman mahukuntan daular Bani Umayyah da suka yi wa iyalan gidan manzo kisan gilla da mabiyansu.

An haifi Said bin Jubair a cikin shekara ta 45 bayan hijira a garin Kufa na Iraki, a lokacin halifanci Imam Ali (A), ya kasance mafi ilimi a tsakanin sauran jama'a a lokacinsa.

3582062

captcha