Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hla da jama’a a ma’aikatar kula da harkokin addini cewa, Hojjatol Islam Ali Muhammadi shugaban hukumar a ganawarsa da babban malamin addini a birnin Qom Ayatollah Ozma Nuri Hamedani, ya bayyana shirin da aka yin a daukar nauyin gasar kur’ani ta duniya.
Wannan gasa dai za ta kebanci mata ne zalla mahardata da makarnta kur’ani mai tsarki daga kasashen duniya daban-daban, gasar dai za ta dauki tsawon mako guda ana gudanar da ita a birnin Tehran babban birnin jamhuriyar muslunci.
Haka nan kuma ya bayyana cewa gasar za ta hada bangarori daban-daban na karatu da harda, da kuma sanin hukuncin karatun kur’ani gami da tafsiri, kamar yadda kuma za ta hada da wasu lamurran na daban, da suka hada baje kolin kayan fasaha da suka shafi kur’ani mai tsarki.
Wannan gasa dai za ta samu halartar makaranta da mahardata mata daga kasashe 74 n duniya, kuma za a dauki tsawon mako guda ne a jere ana gudanar da ita, kamar yadda kuma za a gabatar da makaloli kimanin 100 daga mahalrta taron.
Daga karshe za a bayar da kyatuka ga dukkanin mahalarta gasar, kamar yadda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazoa dukkanin bangarorin gasar, da hakan ya hada da gasar makaloli kan ilmomin kur’ani.