IQNA

Ana Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewa Da Hukuncin Hana Hijabi Turai

23:49 - March 15, 2017
Lambar Labari: 3481315
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da nuna rashin amincewa da hukuncin da kotun kolin tarayyar turai ta dauka na hana musulmi mata saka lullubi a wuraren aiki.

BKamfanin dillanicn labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin Muslims News cewa, ana ci gaba da nuna rashin amincewa kan hukuncin hana mata musulmi saka hijabin muslunci wato lulubi a kawunansu da kotun tarayyar turai ta fitar

Wannan mataki na ci gaba da fuskantar kakakusar suka domin kuwa kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a nahiyar turai da ma wasu kasashen duniya suna ganin hakan ya sabawa tsarin tarayyar turai.

Wannan mataki dai ya zo sakamakon wata takkadama kan korar wasu mata biyu a kasashen Faransa da Belgium kan saka lullubia kansu da suke yi a wurin aikinsu.

Daga bisani kotun koli ta tarayyar turai ta shiga gudanar da bincike kan lamarin, inda daga karshe a jiya ta yanke hukuncin cewa kamfanonin suna da hakkin su hana mata msuulmi masu lullubi yin aiki.

Musulmi suna fuskantar matsaloli da dama a cikin kasashen nahiyar turai musamman mata daga cikinsu da suke saka lullubi a kansu, inda kuma wannan mataki da kotu ta dauka shi ne irinsa na farko a tarihin kasashen turai.

3584501
captcha