Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun daga daren jiya aka fara gudanar da tarukan tunawa da zagowar ranar haihuwar Sayyidah Fatima (SA) a yankunan kasar Pakistan, da hakan ya hada da biranan Karachi, Bishawur, Lahur da kuma Kuita.
Wadannan taruka dai an gudanar da su ne a masallatai da kuma cibiyoyin ilimin addinin mulsunci, inda aka gabtar da jawabai wanda malamai da masana suka gabatar, tare da halartar dubban musulmi.
An gabatar da jawaban da aka yi a cikin harsunan urdu da kuma farisanci, bisa ga al’ada akan kwashe tsawon makon ne ana gudanar da wadannan taruka a dukkanin yankuna na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.