Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, babban alkalin jahar Texas Ken Paxton ya sanar da cewa, matakin da Trump ya dauka na hana musulmi daga wasu kasashe shiga cikin Amurka mataki ne mai kyau, domin hakan a cewarsa zai kara kare rayuwarsu daga barazanar ‘yan ta’adda.
Tun bayan da Trump ya dare kan shugabancin Amurka dai ya sanya hannu kan dokar hana musulmi daga kasashe bakwai shiga Amurka, amma wani babban alkali a wata kotun jahar Washington ya soke dokar, Trump daga kara a wata kotun daukaka kara a San Francisco, amma kotun ta tabbatar da hukuncin da alkali na farko ya zartar na haramta dokar.
Daga bisani kuma Trump ya sake sanya hannu kan wata sabuwar dokar, duk kuwa da cewa ya cire Iraki daga cikin kasashe 7 na farko da ambata, inda dokar ta shafi musulmin kasashen Yemen, Sudan, Iran, Somalia, Libya, Syria, dokar da ita ma wasu alkalai na kasar suka yi watsi da ita.
Tun kafin ya dare kan shugabancin Amurka, Trump ya yi kaurin suna wajen nuna tsananin kyamar musulmi, da kuma shan alwashin shiga kafar wando daya da su matukar ya lashe shugabancin Amurka, duk kuwa da cewa yana mu’amala da wasu daga cikin kasashen musulmin da Amurka ke da maslaha tattare da hakan.