Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, gungun mabiya addinin buda masu tsatsauran ra'ayi sun kaddamar da farmaki da makamai a kan wani gida na musulmi, inda suka kasha iyalan gidan baki daya a yankin Arakan.
Bayanin ya ci gaba da cewa, daga cikin wadanda aka kasha kuwa har da wani karamin yaro da bai wuce shekara guda da haihuwa ba, wanda shi ma suka daddatsa shi da adda.
Wani dan uwan iyalan da aka yi wa kisan gilla ya bayyana cewa, abin da yafaru ba boyayye ne ba, amma gwamnatin kasar ta Myanmar gami da jami'an tsaron kasar sun yi gum da bakunansu, wanda hakan ke nuni da cewa suna da hannu abin da yake faruwa, ko kuma sun amince da hakan ta ci gaba da faruwa.
Musulmin kasar Myanmar dai suna fuskantar kisan kiyashi daga jami'an tsaron gwamnati da kuma mabiya addinin buda masu tsatsauran ra'ayi na kasar.
Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana abin da ya faru na kisan kiyashi a kan musulmi a kasar Myanmar da cewa laifukan yaki ne, kuma jami'an tsaron kasar na hannua cikin hakan.