Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Yens Spahan mataimakin ministan harkokin tattalin arzikin kasar Jamus ya bayyana cewa, dole ne a sanya ido kana bin da ake gudanarwa a cikin masallatai.
Ya ce babban abin da ke da muhimamnci shi ne a san abin da ake yi da kuma abin da ake gaya ma jama'a a cikin hudubobi a masallatai, domin hakan yana da alaka da batun tsaroa kasar.
Kamar yadda kuma ya bukaci da a zauna limamai domin samun karin haske kan dukkanin ayyukansua masallatai da sauran cibiyoyin addini.
Kasar Jamus ta dauki wannan matakin ne domin sanin abin da Turkiya take kitsawa, musamman bayan da aka shiga takun saka tsakanin Jamus da kasar ta Turkiya, inda Jamus ke zargin cewa Turkiya tana tunzura musulmin kasar wadanda akasarinsu turkawa ne domin gudanar da ayyukan ta'addanci.
3586181