IQNA

Birnin Darmashtat Na Jamus Zai Dauki Nauyin Makon Kiyaye Dabi’a

23:43 - April 01, 2017
Lambar Labari: 3481367
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taro na makon kare dabi’a a kasar Jamus.

Kamfanin dillancin iqna ya habarta cewa, kamar yadda aka saba gudana da taruka kan abin da ya shafi dabi’a a kasar Jamus, a wannan karon ma za a gudanar da rin wannan taro, wanda zai mayar da hankali ne kan mahangar addinai dangane da hakan.

Bayanin ya ci gaba da cewa, ofishin jakadancin kasar Iran a kasar ta Jamus zai dauki nauyin gudanar da taron a wannan karo, tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin dabi’a da kuma yanayi ta kasar.

Taron wanda zai gudana a cikin a karshen wannan wata, za samu halartar malamai daga adinai daban-daban, da kuma masana da za su gabatar da jawabai kan matsayin dabi’a a mahangar addinansu. 

A addinin musulunci dabi’a tana da matsayi na musamman, wanda hakan ne ya sanya ake bayar da muhimamnci matuka ga abin da ya shafi rayata domin tana tafiya ne tae da rayuwar bil adama.

Misalin hakan kuwa shi ne, yadda muslunci ya hana a sare itatuwa bbu gaira babu sabar, musamman ma wadanda aka dasa su a wuraren da mutane suke rayuwa, inda muslunci ya hana a kasha tsofi da mata da kananan yara a lokacin yaki, haka kuma ya hana a sare itatuwa koda kuwa a garin amkiya ne da suke yakar muslinci ne.

3586122


captcha