IQNA

An Yi Wa Yaran Baghdadi Kawanya A Mausul

22:49 - April 02, 2017
Lambar Labari: 3481370
Bangaren kasa da kasa, Sojojin kasar Iraki na ci gaba da nausawa zuwa bangaren yamacin birnin Mausul, yankin da a halin yanzu shi kadai ne ya rage a karkashin ikon 'yan ta'addan ISIS a cikin birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, dakarun na Iraki da kuma sauran sojin sa kai na al'ummar kasar, sun kammala tsarkake mafi yawan yankunan birnin mausul da kewa daga 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS, yanzu bangaren yamma maso arewacin birnin kawai yake a karkashin ikon 'yan ta'addan.

Rundunar sojin Iraki ta ce mayakanta suna yin taka tsantsan matuka wajen fatattakar 'yan ta'addan ISIS a wannan yankin, domin kuwa akwai dubban daruruwan fararen hula da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a wurin.

A jiya Asabar wasu 'yan ta'addan ISIS fiye da 200 a cikin motoci 40 sun shigo yankin Talafar da ke tsakanin mausul da kuma iyakokin Iraki da Syria, domin kai dauki ga 'yan ta'adda a Mausul, amma dakarun Iraki sun kashe su baki daya.

3586296

captcha