Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin premium times cewa, kakakin rundunar 'yan sanda ta jahar Bornon ya fadi a safiyar yau Asabar cewa, wasu mata guda biyu dauke da jigidar bama-bamai sun yi yunkurin shiga cikin masallacin babbar kotun jahar da ke Maiduduri, amma jami'an tasron sun hana su, a nan take daya daga cikinsu ta tarwatsa kanta, inda su biyu suka mutu, yayin da mutane biyar da ke wurin suka samu raunuka.
Rahotonni sun tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne a lokacin sallar asubahin yau Asabar, kuma tuni jami'an 'yan sanda suka killace wurin tare da hana jama'a shiga.
Bayanai sun tababtar da cewa ‘yan ta’addan na Boko Haram suna sajewa da sauran mutane domin samun damar kai hare-haren ta’addanci a cikin jama’a maimakon kai hare-hare da suke yi da bindigogi a cikin birnin lokutan baya.
Tuni mahukuntan a Najeriya suka sanar da cewa sun dakushe kaifin ayyukan kungiyar duk kuwa da cewa a cikin loutan baya-bayan nan tana yunkurin sake nuna samuwarta.