Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na Daily journal ya bayar da rahoton cewa, wannan daliba musulma ta gayyaci sauran dalibai da suke aji daya da ita domin yi musu bayani kan matsayin hijabia muslunci.
Baya ga daliban ajin nasu, wasu daga cikin dalibai ma da abin ya burge sun halarci wurin, domin jin abin da take fada, yayin da wasu daga cikinsu musamman ma mata suka saka hijabin suna daukar hotuna,inda suka yaba matuka da abin da ta yi.
A cikin irin bayanin da ta yi musu, ta bayyana musu cewa hijabi a awurin musulmi wani bangaren ne na addini, domin kuwa umarni na addini ga kowace mace musulma
Ta ci tgaba da bayyana cewa, wasu suna kallon mata musulmi masu saka hijabi a matsayin wasu mutane na daban, alhali ba haka ba ne, su daidai suke da kowa, bannacin kawai na fahimta ne.
Ta ce ya kamata masu mummunan tunani kan musulmi musamman mata masu saka hijabi su sauya tunaninsu maimakon gaba da kyama ya kamat su zama abokai masu kaunar juna da dukkanin mutane baki daya, musulmi ne ko ba musulmi, masu saka hijabi ne ko ba masu saka hijabi ba.