IQNA

Takarda Mai Dauke Da Rubutun Kur’ani Shekaru Dari Shida A London

23:32 - April 15, 2017
Lambar Labari: 3481409
Bangaren kasa da kasa, za a nuna wata takarda da take dauke da rubutun kur’ani mai tsarki domin sayar da ita a birnin London.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yam sabi cewa, wannan fallen takarda wanda yake komawa zuwa ga karni na goma sha hudu miladiya, ya dauke ne da rubutun ayoyin kur’ani mai tsarki, da kuma Karin bayani a cikin harshen Indiyanci.

Kimar wannan fallen takarda zai kai kimanin dalar Amurka dubu 5 zuwa dubu 7 kamar yadda aka kiyasta, wanda kuma ana sa ran za a fitar da wanann takardar zuwa bainar jama’a domin sayar da ita.

Akwai wasu daga cikin kayan tarihin muslunci da suka jima a cikin kasar Birtaniya wadanda suke komawa zuwa karnoni masu yawa a baya, wadanda ake ajiye da su ko dai a hannun jama’a a daidaiku, ko kuma a wuraren ajiye kayan tarihi na kasar.

Da dama daga cikin kayan tarihin muslunci da ake ajiye da sua cikin gidajen ajiye kayan tarihi na kasar dai suna da alaka ne da kayan tarihi da’yan mulkin mallaka suke sacewa a kasashen musulmi, ko kuma kasashen da suka yi wa mulkin mallaka.

589722


captcha