IQNA

Gasar Yin Gyara Kan Rashin Fahimtar Kur’ani A Masar

23:14 - May 07, 2017
Lambar Labari: 3481491
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta shirya wata gasa wadda za ta mayar da hankali ga bincike kan abubuwan da ake yin kuren fahimtarsu a kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Al-shuruq cewa, a ciki gaba da hankoron ganin an kyauata lamarin fahimtar addini ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta shirya wata gasa wadda za ta mayar da hankali ga bincike kan abubuwan da ake yin kuren fahimtarsu a kur’ani mai tsarki.

Wannan gasa dai za ta mayar da hankali a kan lamurra da suka zo cikin kur’ani, wanda kuma a kan samu sabanin fahimtar su a wasu lokuta sakamakon yawan mabanbantan ruwayoyi da kuma maganganu na malamai.

Daga cikin wadannan abubuwa kuwa har da salla da kuma aikin hajji yadda ake gudanar da shi da kuma wasu lamurra da suka shafe shi wadanda kur’ani ya ambata, kamar yadda hakan kuma zai hada har da batun azumi da zakka, sai kuma alakar musulmi da sauran addinai musamman addinin kiristanci, da kuma yadda mahangar kur’ani take dangane da shi.

Malamai da daliban ilimi masu bincike ne daio suka shiga cikin wannan gasa, inda suke ci gaba da gudanar da bincike da kuma tattara abubuwan da suka fahimta a mahanga ta ilimi bisa dogaro da irin hujjojinsu.

An fara gasar tunkwanaki biyu dsa suka gabata, kumaza aci gaba da gudanar da ita har zuwa tsawon kwanaki goma, inda daga karshe za a bayar da kyautuka ga wadanda suka fi nuna kwazo, mutum na farko zai samu kyautar fan dubu30 na Masar, na biyu kuma fan dubu 20, sai na uku fan dubu 10.

3596879

captcha