Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sanadarwa na afrigatenews.net cewa, babbar cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a birnin Tripoli na Libya ta bayar da umarnin kwace kwafin kur'anai masu dauke da kura-kurai tare da hana yaduwarsu a kasar.
Tuhami Zaituni shi ne babban darakta na wannan cibiya, ya bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne bayan gano cewa, akwai kwafin kur'ani da ake yi ta hanyar scan, wanda yakan bayyana da kura-kurai kuma a haka ake amfani da wadannan kur'anai a kasar.
Ya bisa la'akari da babban gadarin da yake tattare da hakan, sun dauki matakin tattara kur'anai da aka samar da su ta hanyar kwafi na scan, kuma tuni suka aike da sakonni zuwa ga cibiyoyin da suke harkar kurni da suka hada da makarantu da sauransu, da kuma masu sayarwa.
Bisa ga wannan rahoto cibiyoyin kur'ani Darul Quba, Darul Madinah, Darul manar, Darul Alamiyyah, da Darul Baitul hamd, sai kuma darul Huda wal Iman, da kuma Darul Hijrah, suna daga cibiyoyin da ke buga kur'anai da kuma sayar da su, wadanda suke yada wannan kwafin kur'ani a cikin kasar.
3597228