IQNA

Karuwar Kyamar Musulmi Da Kashi 56 Cikin Dari A Amurka

20:21 - May 09, 2017
Lambar Labari: 3481499
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar musulmi a kasar Amurka ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewa kyamar musulmi ta karu a kasar a cikin wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta fitar, ta tabbatar da cewa a shekara da ta gabata, an aikata laifuka na cin zarafin musulmi tare da nuna musu kyama har sau 2213, a cikin shekara ta 2016.

Rahoton ya ce idan aka kwatanta wadannan ayyuka na shekarar da ta gabata, da kuma ayyukan cin zarafi da nuna kyama ga musulmia cikin wannan shekara a cikin kasar Amurka, ayyukan sun karu da kashi 56 cikin dari, duk kuwa da cewa ana cikin rabin farko na shekarar bana.

Cibiyar musulmin Amurka ta ce wannan yana faruwa ne sakamakon irin matakan da sabbin mahukuntan kasar Amurka suke dauka a karkashin salon siyasar Donald Trump ta kin jinin musulmi, inda hatta jami’an hukumar tsaro ta FBI na suna tsananta ayyukansu a halin yanzu a kan musulmi a kasar.

3597820


captcha