IQNA

Karbala Na Shirin Karbar Baki Msu Ziyarar Nisf Sha’aban

20:24 - May 10, 2017
Lambar Labari: 3481500
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan a birnin Karbala na kasar Iraki sun ce sun yi tanadi dangane da masu ziyarar Nisf Sh’aban.

Kamfanin dillanbcin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyoyin da ke kula da hubbarorin Hussain (AS) da Abbas (AS)sun cewa an kammala dukkanin shurye-shirye domin tarbar masu ziyara a cikin wadannan kwanaki masu albarka.

Adnan Daif shi ne shugaban kula da bangaren tsaro na hubbarori biyu a Karbala, y ace yanzu haka jami’an tsaro sun daukidukaknin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu ziyara,a tsakanin hubbarorin da kuma sauran tituna masu isa wurin.

Haka na kuma ya kara da cewa, baya ga jami’an tsaro masu sanye da kayan sarki, akwai jami’an tsaro na farin kaya, gami da kamarori da aka sanya a dukkanin bangarori da tutuna masu isa hubbarorin biyu masu tsarki, domin tabbatar da ana sanya ido kana bin da ke kai da komowa.

3598123


captcha