Kamfanin dillanin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo radionz cewa, a daren jiya mabiya addinin buda sun kaddamar da farmakia kan msulmi a yankin Rangon, amma jami'an tsaro sun tsarwatsa su ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan mataki ya zo ne sakamakon irin damar da 'yan addinin buda masy tsatsauran ra'ayi suka samu ne daga mahukuntan kasar, inda suke kasha musulmi ba tare da wani abu ya faru da su, ta yadda hatta jami'an 'yan sandan sukan yi hakan tare da su.
Jami'an 'yan sandan dai sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma harba harsasai a cikin isaka, lamarin da ya tsorata 'yan addinin buda masu tsatsauran ra'ayi suka ja da baya.
Maharan dai sun kai farmaki ne a kan makarantu da kuma masalatan musulmi, suna masu nuna rashin amincewarsu da duk wani aiki na ibada da musulmi za su gudanar a yankinsu, har sai sun biya haraji.
A kwanakin baya ne jagororon addinin buda suka gindaya wa musulmi sharadin cewa ba za su yi salla a masallaci ko gudanar da wani taro na addini ba sai sun biya haraji, kamar yadda kuma makarantunsu ma dole su biya haraji ga wuraren bauta na buda, in kuma bah aka za a rusa wuraren tare da kona su.